ZUWA GA WAILAS
Daga taskar Mal. Maude Nuhu
Farfesa Ali Isa Fantami GAMJI
Wanga ɗanɗa namu Isa,
Masu saran diddigen sa,
Za ku sara ne ku bar sa,
Don ko Isa khaliƙin sa,
Shi ya zaɓai ba mutum ba ne ba.
In ka so Isa ka so sa,
Ko kasa ɗamba ka ƙi sa,
Ɗanmu Isa ya yi nesa,
Ya zame tamkar ya ƙusa,
ba a san hanyar cire shi ko ba.
Ƴan'uwa na ku matasa,
Ku yi rubutu don yabon sa,
Don fito da irin halinsa,
Duniya duk har ta san sa,
Bai san aikin ta'adda ko ba.
Babu mai cin diddigen sa,
Sai Ɓarayi masu ƙin sa,
Ƴan ta'adda da ke warisa,
Koko don kyawon halinsa,
Harda yahoo boy da bai sake ba.
Ko ka Mai lakabin Farfesa,
Ko ka ce No! ban kiransa,
Ba ka kwace illiminsa,
Ko ka kwace kyan halinsa,
Ba ka canja fadin Ubangiji ba.
Ayyukan NIN sun yi Nisa,
Ko'ina ya zaga Sassa,
Wanda ke kusa ko a nesa,
To ya tashi ya je ya yi sa,
Ɗan ta'addaba zayyi nassaraba.
Ka faɗawa duk magauta,
Kar wurin ƙullin mugunta
Har ya kai ya zam su manta,
Har ka ƙare yin rijista,
Ba su yo kati na ƴan ƙasa ba.
don ya zam kada su yi shagalta,
Tabbatar NIN sun haɗe ta,
Da wayarda su ke riƙe ta,
Don ko za su ci gajiyar ta,
Ba sai an kai ga an rufeba.
In rijistan ya yi zamzam,
Sun yi liking dukkanin Sim,
Babu laifi ko kaɗan sam,
Su yi ta zazzagin ka malam,
Ƙage Zagi ba ƙari suke ba.
Nuhu Muh.d Maude
Comments
Post a Comment