ZUWA GA WAILAS
![Image](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjCillMWaXa4e1mY-pHT5-DYrd6eDpKFaValDy-fVc3g0cNLZmKHLtIV6BHwoZfSTJFahMRLiAYYScTQ0_ZAm1Dm5O1s3y0MY-ORuhuUD8ohU4YF2D_5B1q8gMnosb25BpHAdaNhk7AQak/s1600/1640709211324331-0.png)
Daga taskar Mal. Maude Nuhu Farfesa Ali Isa Fantami GAMJI Wanga ɗanɗa namu Isa, Masu saran diddigen sa, Za ku sara ne ku bar sa, Don ko Isa khaliƙin sa, Shi ya zaɓai ba mutum ba ne ba. In ka so Isa ka so sa, Ko kasa ɗamba ka ƙi sa, Ɗanmu Isa ya yi nesa, Ya zame tamkar ya ƙusa, ba a san hanyar cire shi ko ba. Ƴan'uwa na ku matasa, Ku yi rubutu don yabon sa, Don fito da irin halinsa, Duniya duk har ta san sa, Bai san aikin ta'adda ko ba. Babu mai cin diddigen sa, Sai Ɓarayi masu ƙin sa, Ƴan ta'adda da ke warisa, Koko don kyawon halinsa, Harda yahoo boy da bai sake ba. Ko ka Mai lakabin Farfesa, Ko ka ce No! ban kiransa, Ba ka kwace illiminsa, ...