YADDA ERDOGAN YAZAMA “GWARZO”


Daga: 
Muhammad Qaddam Sidq Isa.

• Turkiyya tafi kowace kasar musulmi kusanci da kasar Israila; itace kasar musulmi ta farko data amince da “halaccin” kasar Israila tun shekarar 1949, shekarar farko bayan da aka kirkirota akan yankin Falasdinu.  

• Tun lokacin alaqa ta qawance ta qullu tsakanin kasashen guda biyu ta fuskokikin diplomasiyya, da tattalin arziqi da kasuwanci har ma da hadin guiwa akan al’amuraan soja da leqen asiri akan wasu kasashen. Turkiyya tana daya daga cikin manyan kwastomomin da suke siyan makamai daga Israila, kuma malaman sojoji na Israila sun horar da sojojin Turkiyya. Kuma saboda karancin fadin sararin samaniyar kasar Israila, Israila takasance tanayin amfani da sararin samaniyar Turkiyya saboda yin atisayen sojojinta na sama kasancewar babu wata kasar larabawa da sukeda iyaka da Israila da zata amince hakan ya faru akan kasar ta.

• Tafuskar kasuwanci kuwa, har ta kai an samar da yarjejeniyar Free Trade taskanin kasashen guda biyu wanda haka ya habaka kasuwanci taskaninsu.  

• A shekarar 2005 Erdoğan yakai ziyara Israila inda akayi masa girmamawar da har aka kaishi ya dora flower ta girmawa a gurin da aka ware saboda girmama yahudawa da Hitler ya kashe a yakin duniya na biyu. 

• A shekarar 2006, shima Prime Minister Israila Shimon Perez yakai irin wannan ziyara Turkiyya inda akai masa girmamawar da har yayiwa majalisar kasar jawabi. 

• Koda yake Turkiyya ta samu cigaban tattalin arziqi karkashin Erdoğan, a wajejen shekarun 2008, Erdogan ya fara sha’awar yin amfani da musulunci don farfado da tagomashin kasar sa a cikin kasashen larabawa. Kuma kamar ko wane dan siyasa mai irin muradinsa, ya fara da yawan yin bayanai masu nuna tausayawa sosai akan Falasdinawa. 

• Haka ya haifar da musayar harshe wasu lokutan tsakaninsa da Israila wanda hakan yasa wasu musulmi suka fara yi masa kallon wani gwarzo. 

• Har sai shekarar 2011 bayan da Israila ta kashe wasu Turkawa da suke kokarin kai kayan agaji Gaza, sannan ne Erdoğan ya bayyana rage yauqin qawancen dake tsakanin kasar sa da Israila saboda ta kashe Turkawa amma kuma yana nuna saboda Falasdinawa ya dau wannan matakin. 

• Amma kasashen biyu sunci gaba da tattaunawa akan yadda zasu shirya, kuma suka tsara cewa shi Prime Minister Israila Benjamin Netanyahu zai fito ya karbi lefin kisan Turkawan shi kuma Erdogan zai amince, shikenan Magana ta wuce; haka kuma akayi.

• Erdogan yaci gaba da irin wadannan bayanai nasa marasa tasiri a zahiri akan goyon bayan Falasdinawa, da kuma goyawa tarzomar da ta barke a wasu kasashen larabawa a 2011 inda ya goyawa kungiyar Muslim Brotherhood mai tarzoma baya musamman a kasar Masar da Tunusia.   

• Abin yaafi qamari tun lokacin da sojoji suka hambarar da mulkin Muslim Bortherhood a Misra karkashin Muhammad Mursi a 2013, inda Erdogan ya budewa Misra wuta da bayanai masu zafi ya kuma bude kasarsa ga shugabannin Brotherhood din daga Misra da sauran kasashe; yabasu dama suka bude kafofin watsa labaran da basu da aiki sai cin mutuncin gwamnatocin kasashensu da kuma kwarzanta Erdogan a matsayin “Gwarzo” 

• Wannan kwarzantawa tasamu tagomashi sosai sakamakon yadda gidan Talabijin na Aljazeera ya rungumeta ka’in-da na”in. Kasancewar gidan Talabijin ne wanda shima yayi amfani da kamfen irin na Brotherhood don samun karbuwa, kuma saboda karfinsa, yayi nasara sosai wajen halitta gwarzantaka ga Erdogan acikin al’ummomin musulmi. 

• Erdogan yaci gaba da amfani da bayanai na nuna goyon baya ga musulunci a gurare daban-daban amma babu wani abu da yacanja da zai nuna haka a manufofin kasar sa. Yana amfani da musulunci wajen yaqar abokan hamayyarsa na siyasa ni ciki da na waje. Lokacin da alaqa tayi tsami tsakaninsa da France saboda sabanin muradun kasashen a watandar da sukeyi da Syria da Libya, da kuma sabaninsu akan haqar Gas a iyakar cikin tekun Mediterranean bangaren Cyprus da Greece, Erdogan yayi amfani da maganar zanen batanci da akayiwa Annabi (SAW)  akasar wajen yaqar France a diplomisiyyance. 

• Amma abin mamakin shine yadda yake yin bayanai masu cin karo da juna akoyaushe amma masu kwarzantashi kamar basa gani. Misali a dai dai lokacin da ko yaushe in zaiyi bayani ga al’ummar musulmi yake bayyana kansa matsayin mai kishin addini, wani lokacin ma aganshi yana karatun al’qur’ani ko makamancin haka, amma kuma a tarurrukan kasashen duniya yana yawan maimaita cewa shi kasar sa fa ba ruwanta da addini; shi kasar sa “secular” ce kuma akan haka zata dawwama. 

• Kuma haka abin yake a zahiri ma, domin babu wata maa’shaa’a wacce doka ta yadda a aikata ta a kowace kasar Turai wacce ba halattaciya bace a Turkiyya. Har kungoyoyin masu tallata auren jinsi aTurkiyya, kawai yana adawa dasu ne saboda dalilai na siyasa domin babu wani hobbasa da yayi na haaramtasu. 

• In muka koma kan Falasdinawa, a cikin yakoki guda 7 da kasashen Larabawa suka gwabza da Israila, babu lokacin da Turkiyya ta taimakawa Falasdinawa; shi yasa kusan kowace kasa ta larabawa tanada sojoji da suka rasa ransu a gwabzawa da Israila, amma Turkiyya, duk da ba balaribiya bace, alaqar musulunci bata sa ta taba shiga ba. 

• Amma kuma ita Turkiyya babbar member ce a kungiyar hadin kan tsaro ta kasashen Turai da America da Canada wato NATO. Hasalima dai banda America babu kasar data fitata yawan sojoji a kungiyar. 

• Kuma Turkiyya bata taka wata rawar da tadace da matsayinta akan taimakawa da kudaden da ake tattarawa wanda dasune ake daukar nauyin rayuwar miliyoyin Falasdinawan da suke yankin da kuma wadanda suke watse a kasashen duniya. Wanda albarkacin wannan taimako ne yasa duk da barazanar tsaro da Falasdinawa suke fuskanta amma rayuwarsu tafi inganci akan rayuwar ‘yan kasashe da yawa har da Nigeria, a misali.

Comments

Popular Posts